Contact Info

Bayanai Gami da Bidiyo da Kuma Hotunan Sabon Wajen da Ake Kawatawa Domin Saka Sababbin Injinan da Zasu Fara Aiki a Kamfanin Afuwa Welding Works.

Tun a karshen shekarar da ta gabata ta 2022 muka fara kyankyasamuku kamfanin Afuwa Welding Works zai kawo sababbin injinan sarrafa karfe da babu irinsu a kamfanin.

Wannan da kuke gani bidiyon wannan sabon waje ne da ake ginawa kamar yadda idonku ya ganemuku.

Kamar yadda ake gani wannan itace farfajiyar da za a saka wadannan injina.

Haka zalika ana ci gaba da kerawa da kuma kawata wannan waje domin bin komai a sannu wajen saka sababbin injinan da za a kawo.

Haka zalika al’umar Najeriya zasu sha mamaki biyo bayan yadda wannan kamfani zaici gaba da sharemusu kukansu ta fannin kirkira da kuma kere-kere cikin salon fasahar zamani.

Send:

Leave a Reply