Contact Info

Bayanai Dangane da Yadda Kamfanin Afuwa Welding Works Yaje Yayi Aikin Saka Fayif na Ruwa a Sassan Jihoshi Najeriya.

Bayanai Dangane da Yadda Kamfanin Afuwa Welding Works Yaje Yayi Aikin Saka Fayif na Ruwa a Sassan Jihoshi Najeriya.

 

Kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works ya kwashe shekaru da dama yana yin aikin saka fayif (Pipe) na ruwa a sassan jihoshin kasar Najeriya.

Hakan ya samo asali ne tun shekarar 1997 da Eng. Mustapha A Sani ya kafa wannan kamfani kuma yake gudanar da ayyukan sarrafa karfe kala daban-daban.

Wannan kamfani dai ya gudanar da ayyukan saka fayif na ruwa a mafiya yawa jihoshin Najeriya, amma daga ciki zamu fara ambatar wasu jihoshin da guraren da aka gudanar da ayyukan.

A Obajana wajen da attajirinnan da babu kamarsa a nahiyar Afrika akwai babban aikin saka fayif na ruwa da kamfanin Afuwa Welding Works ya gudanar wajen shekaru sama da 10 da suka gabata.

Haka zalika a yayin gudanar da aikin tabbas an yabawa kamfanin Afuwa Welding Works And General Metal Construction wajen yin aiki mai nagarta da inganci, biyo bayan yadda haryanzu aikin bai taba samun tasgaro ba.

Haka zalika a can a jihar Taraba a Mambila, wannan kamfani ya gudanar da manya manyan ayyukan saka fayif na ruwa musamman a wajen gonar nan ta ganyen shayi.

A yayin gudanar da aikin kamfanin Afuwa Welding Works ya yi amfani da salo gami da basira wajen yin aikin kuma tabbas an samu nasarori a ayyukan da aka gudanar.

Muna yiwa masu karatu albishir da cewa ragowar jihoshi da guraren da kamamin Afuwa Welding Works ya gudanar da ayyukan saka fayif na ruwa nan gaba zasu kalli tattaunawa kai saye a bidiyo tare da Engineer Mustapha A Sani wato Managing Director na wannan kamfani domin lisafa sauran jihoshi da guraren da kamfaninsa ya gudanar da aauran ayyukan.

Send:

Leave a Reply