Contact Info

Bayanai Dangane da Sabuwar Fasahar da Shugaban Kamfanin Afuwa Welding Works Yazo da Ita Kamfaninsa Gami da Ingancinta.

Bayanai Dangane da Sabuwar Fasahar da Shugaban Kamfanin Afuwa Welding Works Yazo da Ita Kamfaninsa Gami da Ingancinta.

 

Daga Afuwa Welding Works Media Team.

Tun bayan dawowar shugaban kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works General Metal Construction Engineer Mustapha Abdullahi Sani daga kasar China kamfaninsa ya sake zuwa da sabon salo.

Kamar yadda ya saba fito da sababbin abubuwa gami da kirkirar fasahar zamani domin yin ingantattun ayyuka na zamani gami da salo na musamman.

Tuni wannan kamfani ya fito da fasahar yin zane ko rubuta suna a jikin abubuwan da suka shafi karfe ko leda ko dutse da sauransu.

Yanzu dai akwai manyan guraren da aka fitarmusu da abin saka makulli na karfe (Key Holders) gami da sunayen guraren nasu.

Kamar yadda ake gani Marhaba Store ma anyimus wannan abu a tsakiyar makonnan.

Haka zalika suma albarka Store anyimusu wannan abu kamar yadda ake kallo ga sunayennan a jiki.

Kuma wannan karfe da kuke ganin anayin wannan abu dashi karfe ne da mayen karfe baya hawansa kamar yadda ake ganinsa yana kyalli.

Yayin tattaunawa da Eng. Mustapha Abdullahi Sani ta www.afuwaweldingworks.com dangane da wannan sabuwar fasahar ya bayyana cewar wannan itace tsarabar farko ta wannan inji na Fiber Laser Marking Machine kafin manyan tsarabar su karaso. Haka zalika a lokacin da akai hira da Eng. Mustapha A Sani a gidan rediyon Premier 102.7 f.m a karshen makon da ya gabata suma ya kaimusu tsarabar key holders da sunan gidan da kuma mitar gidan rediyon.

Haka zalika akwai mutane da dama da akayimusu wato aka rubutamusu sunansu ko kuma wata inkiya.

Sannan akwai wadanda aka fitar aka rangada sunan kamfanin Afuwa Welding WorksAfuwa Welding Works  gami da sauran wasu muhimman abubuwan.

Daga karshe muna bayyanamuku cewar wannan mashin din ankawoshi ne domin sharewa kwastomomi hawaye kuma daga ko ina suke zasu iya garzayowa kamfanin domin a fitarmusu da sunan da suke da bukata.

Send:

Leave a Reply