Contact Info

Bayanai da Jawabai Akan Birnin Gounzou Gami da Guraren da Eng. Mustapha A Sani yake Ziyarta a Tafiyar da Yayi Zuwa Bikin Bajakoli a China.

Bayanai da Jawabai Akan Birnin Gounzou Gami da Guraren da Eng. Mustapha A Sani yake Ziyarta a Tafiyar da Yayi Zuwa Bikin Bajakoli a China.

 

Birnin Gounzou ya kasance a bangaren Kudancin kasar China, kuma ana kiransa da suna Canton. Wannan birni ya kasance birnin Guangdong.

Sannan wannan birni na Ghounzou ya kasance kusa da kogin Pearl kimanin Kilomita 120 daga Arewa Maso Yammacin Hong Kong.

Wannan birni yana da tarihin shekaru Dubu Biyu da Dari Biyu (2,200) da kafuwa a kasar ta China.

A kidayar da aka gudanar a shekarar 2020 anyi ittifagin akwai mutane 18,676,605.

Tuni dai shugaban kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction wato Engineer Mustapha A Sani ya sauka a wannan birni kuma ya fara ziyartar manyan guraren sayar da injina.

Wannan birni dai Engineer Mustapha Sani ya saba zuwansa domin huldar kasuwancinsa domin ya sha zuwa a shekarun baya.

Kamar yadda ake ginin hotunan Engineer Mustapha Abdullahi Sani a wasu gurare na musamman da kuma wasu kamfanoni tare da mutanen kasar ta China.

A yanzu haka kamar yadda kuke gani Mustapha Afuwa yana ta ziyartar manyan gurare a birnin na Ghounzou kafin lokacin dawowarsa Najeriya.

Wannan birni na Ghounzou dai ya kasance mai tsohon tarihi, ga wasu kauyuka da aka sake yimusu garambawul zamu zayyanomuku kamar haka.

1. Akwai wajen da ake kira Shawan kuma tsohon kauye ne mai cike da tarihi.

2. Sannan kuma akwai wani karamin kauye mai dimbin tarihi da ake kirnsa da suna Xiaozhou wanda yanzu aka kawata wajen ya zama birbin a yankin Lingman.

3. Akwai kauyen da ake kira da Huangpu wanda shikuma ya bambanta da sauran kauyukan sannan kuma ya bambanta da gine ginen da akayi a birnin na Ghounzou, wajene na musamman sannan kuma wajen babu hayaniya sam.

4. Akwai kauyen da ake kiransa da suna Jinggu, wannan kauye ya kasance yana da tarihin shekaru Dubu (1000) da ginawa, wannan kauye dai yana kusa da tsibirin Huangpu Changzhou.

5. Akwai gini mai tsohon tarihi da ake kiransa da Qing Dynasty a cikin Frangcum a Ghounzou.

6.Sannan cikon na shida akwai kauyen Langtou wanda yake a garin Tambu.

Za muci gaba da kawomuku abubuwa na musamman dangane da ziyarar wannan bikin bajakoli da shugaban kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction halarta a kasar China.

Send:

Leave a Reply