Contact Info

Bayan Kwashe Sama da Kwanaki 10 a Kasar China Eng. Mustapha A Sani ya Ziyarci Muhimman Gurare a Birnin Ghounzou Kamar…

Bayan Kwashe Sama da Kwanaki 10 a Kasar China Eng. Mustapha A Sani ya Ziyarci Muhimman Gurare a Birnin Ghounzou Kamar

 

Shugaban kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction Engineer Mustapha Abdullahi Sani ya kwashe sama da kwanaki Goma (10) a birnin Ghounzou na kasar China.

Wannan birni dai ya kasance shine birni na Biyu (2) da aka fi ji da shi a kasar ta China, kuma shine birnin da ake gudanar da bikin bajakoli lokaci zuwa lokaci.

A wannan kwanaki da Engineer Mustapha Abdullahi Sani ya kwashe a kasar ya ziyarci manyan kamfanonuwan da ake sayar da injina tare da abokanan tafiyarsa.

Haka zalika ya ziyarci kamfanin da ake kera kananan babura na hawa kamar yadda ake ganunsu a babbar ma’ajiya wato (store).

Wannan biki na bajakoli dai duniya ce take taruwa inda mutane suke zuwa daga kasashe daban-daban kuma daga nahiyoyi daban-daban.

Bugu da kari Engineer Mustapha A Sani ya ziyarci guraren wasanni musamman guraren da yara da manya suke gudanar da wasannin nasu.

Wasu kamfanonuwan sun kasance a saman bene mai hawa da yawa ta yadda idan mutum yana kallon kasa zaiga komai da komai a cikin kwaryar birnin na Ghounzou.

Sannan kuma ya ziyarci guraren bude ido a wannan birni musamman guraren da suke da dimbin tarihi kuma ake alfahari da su a kasar ta China.

Wannan tafiya dai da yayi zuwa kasar ta China ta ksance domin sake kawo injinan da zasu sake kawata kwastomomi da ayyukan da babu irinsu musamman yadda kamfaninsa na Afuwa Welding Works And General Metal Construction ya kasance mai aiki da salon fasahar zamani gami da kirkirar adon da babu irinsa.

Send:

Leave a Reply