Contact Info

Barka da Juma’a: Sakon Tunatarwa Dangane da Wannan Rana Ta Juma’a Daga Bakin Shugaban Kamfanin Afuwa Welding Works Alhaji Mustapha A Sani.

Yau ma kamar ko wanne mako wato ranar Juma’a, akwai sakon tunatarwa ga ‘yan uwa Musulmi daga shugaban wannan kamfani.

Kamar yadda Alhaji Mustapha Abdullahi Sani ya saba tunatar da ‘yan uwa ako wanne mako kenan, yau ma ya yi wata tunatarwa.

Tunatarwar dai ta wannan rana dangane da furta magana ce.

“Ina kira ga al’umma idan har zaka furta wata magana da za ta sosawa mutum rai wato yaji babu dadi to kayi shiru shine ya fiyemaka alkhairi”

Alhaji Mustapha Abdullahi Sani ya kara da cewar akwai Hadisi da yayi magsna akan mutum ya fadi alkhairi ko yayi shiru.

Daga karshe Eng. Mustapha Abdullahi Sani ya yi addu’ar Allah Ya hadamu da alkhairan dake cikin wannan rana, Ya karemu da dukkanin sharrin dake cikin wannan rana mai albarka ta Juma’a.

Send:

Leave a Reply