Contact Info

Anaci Gaba da Tafiya Dai Dai da Zamani Gami da Salon Sabuwar Fasaha a Duniyar Kere Kere a Kamfanin Afuwa Welding Works

Kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works naci gaba da tafiya dai-dai da zamani gami da yayi a duniyar kere-kere.

Wannan tafiya da zamani na zuwa ne ta cikin salon sabuwar fasahar zamani a duniyar kere-keren da yake da ruwa da tsaki da karfe.

Haka zalika kamar yadda masu bibiyar shafukan sada zumunta na wannan kamfani suna ganin yadda ake yiwa karfe domin mayar dashi wata siffa ba tare da bata lokaci ba.

A kullum akanga sabon salon aikin da aka gudanar a shafin Tik Tok ko Facebook ko Twitter ko Threads ko kuma Instagram.

A yanzu haka a kusan kowacce rana sai an fitar da wata sabuwar fasaha ko kirkira a kamfanin Afuwa Welding Works And General Metal Construction.

Wani abin sha’awa ma’aikatan ko wanne sashe na wannan kamfani sun kware wajen yin ayyukansu kamar yadda suka samu horo na musamman daga Engineer Mustapha A Sani wato shugaban wannan kamfani na Afuwa Welding Works.

Anaci Gaba da Tafiya Dai Dai da Zamani Gami da Salon Sabuwar Fasaha a Duniyar Kere Kere a Kamfanin Afuwa Welding Works

Send:

Leave a Reply