Contact Info

An Zana Hoton Sarkin Kano Ajikin Karfe a Kamfanin Afuwa Welding Works Wato Alhaji Aminu Ado Bayero C.F.R.J.P

Kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction ya sake gudanar da gagarumin aikin zanen hoton mai martaba sarkin Kano wato Alhaji Aminu Ado Bayero C.F.R.J.P

Wannan zane dai an dauki tsawon lokaci ana gudanar da aikinsa wato wajen yimasa ado da kuma sakamasa kyalakyale kuma zane mai inganci.

Wannan zane dai da aka gudanar a bangaren sarauta a kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works shine Karon farko da aka zana hotonsa.

Fasihin injiniya nan da yayi fice a kasar nan wajen sarrafa karfe wato Eng. Mustapha A Sani shine ya fitar da wannan zane cikin sabon salon fasahar zamani kuma inji ya aiwatar da zanen.

Idan za a iya tunawa kamfanin Afuwa Welding Works ya zana hotunan mashahuran manyan mutane a kasar nan ciki harda manyan ‘yan siyasa da suka hadar ‘yan takarar shugabacin kasar Najeriya da gwamnoni kamar Alhaji Atiku Abubakar da Hon. Khamisu Mai Lantarki wanda yayi takarar gwamna a jihar Gombe da sauransu.

Kamfanin Afuwa Welding Works dai ya yi fice a kasar Najeriya da Afrika baki daya wajen yin ayyuka masu inganci da kuma kitkirar ayyukan da babu irinsu cikin sabon salon fasahar zamani.

Send:

Leave a Reply