Contact Info

Alhaji Mustpha A Sani: Nasiharmu ta Yau Juma’a Gami da Gabatowar Azumin Watan Ramadan.

Tabba dukkanin abin da Allah S.W.A ya sanyawa lokaci to babu makawa sai yazo, domin kuwa ana gaf da shiga Azumin wata mai alfarma wato watan Ramadan.

A wannan rana ta Juma’a wadda ba za a sake shiga wata Juma’arba face wadda za tazo a cikin wata mai alfarma watan na Ramadan.

Kamar kowanne mako da mamallakin wannan kamfani ya saba zuwa da nisiharsa ga ‘yan uwa musulmi ta fannoni daban-daban.

A wannan rana ma Alhaji Mustapha A Sani ya sake yin tunatarwa ga ‘yan uwa musulmi musamman dangane da gabatowar wannan wata mai alfarma da zai kama na Ramadan.

“Nasiharmu ta yau Juma’a ita ce tabbas watan da ake ninka lada ya zo wato watan da Allah ya ke buɗe ƙofofin Rahama ga bayinsa, sabo da haka mu dage da ibada da kuma rubanya ayyukanmu, mu guji dukkanin wasu abubuwa da Allah bayasonsu domin mu samu dacewa”.

” Sannan kuma ina kira ga ‘yan uwa Musulmi akan yadda muke gudamar da ibada lokacin watan Ramadan to ko da watan ya wuce mu ci gaba da yin ibadarmu ba wai muce tunda Ramadan ya wuce bari mu daina, wannan babbam kuskure ne”.

Daga Karshe Alhaji Mustapha A Sani ya yi addua’ar don albarkacin wannan wata da za a shiga mai alfarma Allah ya kawowa ƙasar Najeriya zaman lafiya da kwanciyar hankali albarkacin wannan wata mai alfarma da zai kama na Ramadan.

Send:

Leave a Reply