Contact Info

Alhaji Mustapha A Sani ya Sauka a Kano Bayan Shafe Makonni Biyu Yana Gudanar da Ibadar Umara.

Mamallakin katafaren kanfanin sarrafa ƙarfe nan da babu tamkarsa a wajen yin ayyuka masu inganci wato Afuwa Welding Works & General Metal Construction da ake kira da Alhaji Mustapha A Sani ya sauka a Kano.

Ya sauka a Kano daga can ƙasa mai tsarki a wannan yammaci na Talata bayan ya shafe makonni biyu yana gudanar da aikin Umarah kwanaki 14 kenan.

A yayin tattaunawa da shafin yanar gizo na wannan kamfani Alhaji Mustapha A Sani ya bayyanamana cewar:

“A yanzu haka ina kan hanyata daga Filin Sauka da Tashi na Sarki Abdul Aziz dake Jidda zuwa Kano wato Filin Sauka da tashi na Malam Aminu Kano”

Mustapha Afuwa ya sauka a Kano a wannan yammaci na Talata 2 ga watan Shawwal wanda yayi dai-dai da 3 ga watan Mayu, 2022.

Alhaji Mustapha ya nuna godiyarsa ga Allah da ya saukeshi lafiya sannan kuma ya godewa al’ummar da suka dinga yimasa fatan alkhairi da addu’a lokacin da yake gudanar da ibadar ta Umara.

Send:

Leave a Reply