Contact Info

Alhaji Mustapha A Sani ya Aika Sakon Barka da Juma’a ga Al’ummar Musulmi.

Ranar Juma’a dai rana ce da ake kiranta da babbar rana sakamakon yadda Allah S.W.A ya saukar da albarka a cikinta.

Kamar kowanne lokaci Alhaji Mustapha A Sani ya saba mika sakon barka da Juma’a ga ‘yan uwa Musulmi ta sigogi daban-daban.

A wannan rana ma ya tunatar da ‘yan uwa Musulmi musamman akan kalmar nan ta kyakyawar dabi’a.

Alhaji Mustapha A Sani ya yi kira ga al’umma da su kasance masu kyawun dabi’a a dukkanin inda suka samu kansu.

Haka zalika yayi kira ga iyayen yara da su jajairce wajen cusawa ‘ya’yansu dabi’u na gari da kuma kyawawan halaye domin su zamanto masu nagarta.

Daga karshe Alhaji Mustapha A Sani ya kara kira ga iyaye akan tabbas sai suna sanya idanu akan ‘ya’yansu ako da yaushe musamman a wannan zamanin da ake ciki. Haka zalika yayi addu’ar Allah kawomana sassauci a wannan rayuwar ya kuma bamu shuwagabanni na gari.

Send:

Leave a Reply