Contact Info

Alhaji Mustapha A Sani Naci Gaba da Gudanar da Ibadar Umara a Ƙasa Mai Tsarki

Mamallakin katafaren kamfanin sarrafa ƙarfennan da babu kamarsa a Arewacin Najeriya da ake kira da Afuwa Welding Works And General Metal Construction wato Alhaji Mustapha A Sani naci gaba da gudanar da ibadarsa ta Umara cikin ƙoshin lafiya.

Wannan na zuwa ne bayan da ya kwashe wasu kwanaki a ƙasa mai tsarki inda ya bar Najeriya a ranar Litinin wadda ta gabata kuma ya sauka a ƙasa mai tsarki.

Alhaji Mustapha A Sani yayi fatan alkhairi ga al’ummar Musulmi da Najeriya da jihar Kano baki ɗaya.

Sannan Alhaji Mustapha A Sani yayi kira ga al’ummar Musulmi da su ninka ayyukansu na lada dana ibada a wannan goman ƙarshen da ake ciki ta watan Ramadan, domin Nana Aisha R.A tace: “Manzon Allah S.A.W ya kasance yana ninka ƙoƙarinsa a goman (10) ƙarshe na Ramadan irin yanda bayayi a wani wata wanda ba shi ba”.

Daga ƙarshe ya yi addu’ar Allah ya karbi ibadunmu a wannan wata mai alfarma na Ramadan.

Send:

Leave a Reply