Contact Info

Alhaji Mustapha A Sani: Na Ziyarci Wurare da Yawa a Kasar China Sannan Kuma Ina Furta Maganganu da Yaren Kasar China.

Shugaban kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction ya kasance ya ziyarci wurare da yawa a kasar China.

Alhaji Mustapha A Sani ya sha bayyana hakan a hira da aka yi dashi a gidajen talabijin da gidajen rediyo.

Mustapha Afuwa dai mafiya yawan kayayyakin aikin kamfaninsa duk a kasar China yake zuwa ya siyosu ko kuma ya sa a kirkirarmasa irin wanda yakeso.

“Na kasance inajin yaren kasar China jefi-jefi sakamakon yawan zuwa kasar dana keyi, kuma tabbas na ziyarci gurare da dama kuma tabbas nayi mu’amala da mutanen kasar ta China shekara da shekaru”.

Nan gaba kadan wannan shafi na yanar gizo zai sakarmuku gajerun bidiyo na Alhaji Mustapha A Sani lokacin da yake yin yaren China a wata hira da aka yi dashi.

Send:

Leave a Reply