Contact Info

Akwai Ayyukan da Kamfanin Afuwa Welding Works Yake Gudanarwa Dasu da Hannu Amma Mafiya Yawan Mutane Suna Zaton Inji ne Yake Gudanar Dasu Biyo Bayan Yadda Ma’aikatan Kamfanin Suka Kware Wajen Sanin Aiki.

Akwai ayyuka na musamman da kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works yake gudanar dasu amma mafiya yawan mutane suna zaton cewa da inji ake gudanar dasu.

Ba komai ne ya kawo hakan ba face horo na musamman da ma’aikatan suke samu daga wajen shugaban wannan kamfani wato Engineer Mustapha A Sani.

Ba iya ayyukan hannu ba, hatta wasu injinan da akeyin aiki dasu a kamfanin na Afuwa Welding Works shi da kansa Eng. Mustapha Abdullahi Sani ne ya kirkire su kuma suke gudanar da ayyuka tamkar wadanda ake sayowa daga kasashen waje.

Kamar yadda kuke ganin wannan aikin na waldace wannan karfen da ake gudanar da wannan abin, amma bayan kammala aikin tamkar inji ne ya gudanar da aikin.

Ba’ada bayan haka wannan kamfani ya kasance yafi kowanne kamfanin sarrafa karfe kayan aiki gami da manyan injinan sarrafa karfe a Arewacin Najeriya.

Hakance ta sanya ako wacce jiha a fadin kasar Najeriya akwai ayyukan da wannan kamfani ya gudanar, domin kuwa ga babban misali nan guda daya na ayyukan madatsar ruwa da kamfanin Afuwa Welding Works ya gudanar a Obajana a shekarun baya wato wajen da kamfanin siminti na Alhaji Aliko Dangote yake.

Sannan kuma akwai ayyukan da wannan kamfani yake gudanarwa ake kaisu zuwa wasu kasashen da suke a nahiyar Afrika kamar Chad da Niger da Senegal da Cameroon da sauransu.

Send:

Leave a Reply