Contact Info

A Farkon Watan Janairu 2022 Alan WaƘa ya Ziyarci Kamfani Afuwa Welding Works & General Metal Construction

A farkon sabuwar shekarar nan da muke ciki ta 2022 ranar Litinin 3 ga watan Janairu, 2022 fitaccen mawaƙin Hausar nan Aminu Ala ya ziyarci katafaren kamfanin sarrafa ƙarfe da babu kamarsa a arewacin Najeriya wato Afuwa Welding Works & General Metal Construction.

Shidai wannan katafaren kamfanin wanda yake a kasuwar Ƙofar Ruwa dake jihar Kano kamfanine wanda yake ci gaba da zuwa da salo iri-iri kuma salo mai tafiya da zamani da yayi.

Kamar yadda aka gani mamallakin wannan kamfanin wato Alhaji Mustapha A Sani ya kasance tare da mawaƙi Aminu Ala inda suka tattauna muhimman batutuwa cikin annashawa kuma Aminu Ala yayi masa tambayoyi na musamman shikuma ya bayar da amsa.

Kamar yadda wasu suke tambayar ko menene ya sanya ake ta ganin sashe kala-kala a wannan kamfani? Amsar dai itace wannan kamfani shi kansa a cikin ayyukan sakemasa gini na musamman ake kuma komai ya zai kammala biyo bayan yadda akeci gaba da ƙawata kamfanin.

Kuma a yanzu haka kamfanin dukkanin wanda ya shiga sai yaga ya bashi sha’awa biyo bayan yadda ya ginu sosai da sosai.

Daga ƙarshe shi kansa Aminu Ala ya nuna farin cikinsa dangane da zuwa wannan kamfanin inda ya ya kawo ziyara ta musamman kenan.

Kuma shima yayi addu’ar Allah yaci gaba da ɗaukaka wannan katafaren kamfani na sarrafa ƙarafa da babu tamkarsa a Arewacin Najeriya.

Send:

Leave a Reply