Contact Info

Ɗakin Gari Jihar Kebbi: Yadda Kamfanin Afuwa Welding Works Yayi Aikin Raftocin Ƙarfe a Jihar Kebbi.

Kamar yadda bayanai suka gabata cewar wannan shafi na yanar gizo na kamfanin sarrafa ƙarfe wato Afuwa Welding Works And General Metal Construction ya na ci gaba da yin tariyar baya (Flash Back) dangane da ayyukansa da ya gudanar a kusan dukkanin jihohin Najeriya.

Idan za a iya tunawa a kwanakin baya wannan shafin yanar gizo ya saki labari akan yadda wannan katafaren kamfani ya bayar da gudun mawa wajen saka pipe na Dam ɗin Obajana wato jihar Kogi a lokacin da attajirinnan Alhaji Aliko Ɗangote zai gina katafaren kamfanin siminti, inda wannan kamfani na Afuwa Welding yayi aikin dukkanin magudanan ruwa a lokacin.

To a wannan karon kuma mun tsallaka zuwa jihar Kebbi inda muka sauka a garin nan da ake kira da Ɗakin Gari dake Ƙaramar Hukumar Suru ta jihar Kebbi wato garin da wannan kamfani ya gudanar da raftar ƙarfe (Metal Rapter).

A wannan Ƙaramar Hukumar ta Suru wato inda wannan gari yake da ake kira da Ɗakin Gari wannan kamfani ya yi ayyuka da dama wanda daga ciki akwai raftar ƙarfe kamar yadda muka bayyana.

Domin kuwa ga dukkanin wanda ya san jihar Kebbi kuma ya san garin Ɗakin Gari zai shaida wannan katafaren titin.

Wannan raftar ƙarfe da aka gudanar anyi wasu gine-gine ne a lokacin kuma ginin haryanzu yananna tamkar lokacin da aka yishi sakamakon yadda wannan kamfani na Afuwa Welding Works And General Metal Construction yake gudanar da ayyuka ingatattu.

Jihar Kebbi dai jiha ce wadda a shekarun baya ake kiranta da Arewa Maso Yamma lokacin tana haɗe da jihar Sokoto kafin a sanyawa kowacce sunanta a tsakanin shekarar 1967 zuwa 1976, ana maganar bayan Najeriya ta samu ‘yancin kai daga Turawan Mulkin Mallaka.

Daga shekarar 1976 zuwa 1991 Sokoto ce a matsayin jiha amma ita Kebbi lokacin tana ƙarƙashin jihar Sokoto.

A ranar 27 ga watan Ogusta (August), 1991 aka ƙirƙiri jihar Kebbi inda ake kiran cikin birnin da Birnin Kebbi. Kuma babban abin da jihar Kebbi tafi alfahari dashi shine sana’ar kamun kifi.

Ita kuwa Ƙaramar Hukumar Suru tana daga cikin Ƙananan Hukumomi guda 21 da ake dasu a jihar Kebbi inda take da abin da masana ilimin Geography suke cewa:

Latitude: 11° 38′ 53″ N.

Longitude: 4° 3′ 42″ E.

Lat/Long (dec) 11.64809,4.06177.

Haka zalika a lokacin da aka gudanar da ƙidayar 2016 wannan Ƙaramar Hukumar ta Suru tana da adadin yawan mutane 12,558.

A jihar ta Kebbi dai kamfanin Afuwa Welding Works And General Metal Construction ya gudanar da ayyuka kala-kala inda zamuyi ta kawomuku su a hankali a wannan sashe na yanar gizo na wannan kamfani.

Zaku iya bibiyarmu a shafuka kamar haka:

www.afuwaweldingworks.com

Facebook: Afuwa Welding Works And General Metal Construction.

Twitter: Afuwa Welding Works.

Gmail: mustyabdul63@gmail.com

Lambar Waya: 0802826771

Send:

Leave a Reply