Contact Info

Ƙungiyar Northern Peace Foundation ta Karrama Mamallakin Kamfanin Afuwa Welding Works Mustapha A Sani

Ƙungiyar Northern Peace Foundation ta karrama Mustapha A Sani (Mustapha Afuwa) mamallakin katafaren kamfanin sarrafa ƙarfennan da ya yi shuhura wato kamfanin da babu kamarsa a Arewacin Najeriya wajen kayayyakin aiki na sarrafa ƙarfe wato Afuwa Welding Works And General Metal Construction Company.

Ƙungiyar ta karrama shi ne bisa yadda ya jajirce yake bayar da ilimin ayyuka ga al’umma musamman ma’aikatan da suke zuwa wannan kamfani ƙwaƙwalwarsu tana sake buɗewa da ayyuka na zamani.

Ita dai wannan ƙungiyar ta bayyana cewar hasali ma bata san Mustapha A Sani ba amma kuma yadda su ka bibiyi ayyukan da kamfaninsa yake gudanarwa da rubuce-rubuce a dandalin sada zumunta da kafafan yaɗa labarai da kuma yadda kamfanin yake samawa matasa aikin yi domin hanasu shiga hanyar da bata dace ba da hanasu zaman banza.

Haka zalika ƙungiyar ta ƙara da cewar duba da yadda Ilimi ya yi ƙaranci a Arewacin Najeriya to wannan kamfani tabbas yana bayar da gudun mawa wajen mayar da mutane al’umma mai hangen nesa da tunani mai kyau.

Wannan abubuwa sune suka sanya wannan ƙungiyar maisuna Northern Peace Foundation ta karrama Mustapha A Sani sannan kuma ta bashi lambar girmamawa.

Shi kansa wannan kamfani na Afuwa Welding Works And General Metal Construction ya kan karɓi ɗalibai masu sanin makamar aiki da ake turowa daga jami’o’i daban-daban musamman masu karantar fannin Injiniyanci.

Wannan lambar yabo da karramawa da aka yiwa mamallakin wannan kamfani ba ita ce ta farko ba, a baya ansha karrama shi sosai da kuma bashi lambar yabo daga sassa da dama na ƙasar nan.

Send:

Leave a Reply