Contact Info

Ƙaramar Hukumar Wudil: Ayyukan da Kamfanin Afuwa Welding Works & General Metal Construction ya Gudanar a Ƙaramar Hukumar Wudil

Biyo bayan yadda wannan shafi na yanar gizo yake ci gaba da kawomuku ayyuka kala-kala da ya gudanar a jihohin Najeriya musamma wasu ayyuka na shekarun baya.

A wannan lokaci kuma munzomuku da sababbin ayyukan da wannan katafaren kamfani yake gudanarwa a Ƙaramar Hukumar Wudil dake jihar Kanon Dabo.

Wannan Raftar Ƙarfen (Metal Rafter) da kuke gani an gudanar da ita ne a Ƙaramar Hukumar Wudil wato Ƙaramar Hukuma mai tarihi.

Wannan aiki aiki ne mai inganci da nagarta kamar yadda wannan kamfani ya saba kuma ake yabawa da ayyukan nasa tako wanne fanni.

Wannan ayyuka da kuke gani anyi su cikin nutsuwa da kaifin basira kuma har aka cimma nasara sosai da sosai.

Su kansu mutanen da aka yiwa wannan aiki sun nuna jin daɗinsu da jinjina ga kamfanin Afuwa Welding Works And General Metal Construction.

Ƙaramar Hukumar Wudil ta kasance ana kiranta da Wudil Kana Cibiyar Ruwa, haka zalika tana daga cikin Ƙananan Hukumomin da suke da tarihi kuma ake gudanar da sana’o’i sosai da sosai.

Send:

Leave a Reply